Asabar 6 Yuni 2026 - 16:26
Saƙon Ta'aziyyar Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na Rasuwar Ayatullah Al-Uzma Fayyadh

Hauza/ Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya ya aike da saƙon ta'aziyyar rasuwar babban marja'i, Hazrat Ayatullah Al-Uzma Sheikh Muhammad Ishaƙ Fayyadh.

A cewar rahoton wakilin sashen ƙasa da ƙasa na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, biyo bayan rasuwar babban malami kuma marja'i mai daraja, Hazrat Ayatullah Al-Uzma Sheikh Muhammad Ishayq Fayyadh, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fitar da saƙon ta'aziyya.

Ga fassarar saƙon kamar yadda yake:

Bismillahir Rahmanir Rahim

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un

Muna miƙa ta'aziyyar rasuwar babban marja'in addini, Hazrat Ayatullah Al-Uzma Sheikh Ishaƙ Al-Fayyadh ga manyan marja'an addini, musamman ma na birnin Najaf Al-Ashraf, da daukacin al'ummar Musulmi na duniya. Muna rokon Allah Mai girma da gafarar zunubai da ya sanya shi a cikin faffadan aljannarSa madaidaciya, kuma ya daukaka darajar wannan malami na Ubangiji.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha